ads

Advertising

An yi zanga-zanga kan kama mata masu sa matsatsun kaya a Abuja

Women carry placards
Masu fafutukar kare hakkin bil adama sun gudanar da wata zanga-zangar lumana a Abuja babban birnin Najeriya inda suka nuna rashin jin dadinsu dangane da yadda 'yan sandan kasar ke takura wa mata masu saka matsatsun kaya da ke bayyana tsiraici.
Masu zanga-zangar dai sun fara ne daga tsohon filin pareti (Old Parade ground) har zuwa ofishin 'yan sanda na birnin tarayya da ke unguwar Garki.
Da dama cikin masu zanga-zangar sun dauki kwalaye dauke da rubuce-rubuce inda wasu suka rubuta '' Ni mace ce, kuma ra'ayina ne irin kayan da zan saka.''
Wasu daga cikin matan da aka kama a lokacin samamen da aka kai a wasu gidajen rawa a baya sun zargi 'yan sanda da yi masu fyade a lokacin da suke tsare.
  • Pipo hold placard
Masu zanga-zangar sun bayyana cewa kamen da 'yan sandan suke yi ya sabawa doka da kuma take hakkin mata.
Protest on top abuse of suspected prostitutes for Abuja
Daya daga cikin masu zanga-zangar da ke kare hakkin mata da ta hallarci zanga-zangar Aisha Yesufu ta bayyana cewa dalilin da ya sa ta fito zanga-zangar shi ne ta fadi cewa ''abin ya isa haka.''
Protest on top abuse of suspected prostitutes for Abuja
Aisha ta ce ''Abin ya fara zama kamar mun yi laifi don mu mata ne, suna yi wa mata abin da suka ga dama, mutum na tafiya ko da rana tsaka sai 'yan sanda su kama mutum su saka a mota.''
Women dey protest
Image captionMaza da mata sun fito zanga-zangar
Da dama daga cikin matan sun bayyana cewa abin da ake yi masu ya isa haka nan, suna bukatar 'yan sanda su kare su ba su rinka cin mutuncinsu ba.
Sai dai a na su bangaren, mataimakin kwamishinan 'yan sanda mai kula da ayyukan rundunar Usman Umar ya shaida cewa tuni suka fara gudanar da bincike kan zarge-zargen da ake yi.
Ya kuma bayyana cewa za su ci gaba da aikinsu na kare hakkin duk wani dan kasa ba mata kawai ba.
A kwanakin baya ne dai jami'an tsaron hadin gwiwa suka kai samame wasu daga cikin gidajen rawa a Abuja inda suka ce sun kama mata tsirara suna rawa.

No comments:

Post a Comment